Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto babban komandan sojojin rundunar ta Lake Chad Basin Multi-National Task Force (MNJTF) Manjo Janar Lamidi Adeosun yana fadar haka
Adeosun ya bayyana haka ne a lokacinda yake amsa tambayoyi a taron tattaunawa wanda ma'aikatar tsaron kasar Amurka ta shirye, ta wayan tarho.
Taron karan bayanin dai sami halattar babban komandan sojojin Amurka a nahiyar Afrika ADRICOM, General Thomas Waldhauser, komandan sojojin tarayyar Afrika AMISON Lt. General Osman Noor Soubagleh da kuma wakili na musamman ga kungiyar tarayyar Afrika Ambassador Madeira.
Labarin ya kara da cewa an dauki sautin tattaunawan ne a karamin ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Lagis na Nigeria.288